• Home
  • About
  • Privacy Policy
  • Contact
  • News
  • Politics
  • Business
  • Technology
  • Health
  • Sports
  • Entertainment
  • Product Reviews
  • How To’s
No Result
View All Result
MondayNuggets
No Result
View All Result

Muna taya al’umman musulmai zagayowar watan azumin ramadan — Sakon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres

Monday Yakubu by Monday Yakubu
February 28, 2025
in News
0

Sakatarin Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, yana mika gaisuwar sa ga dukan al’umman musilmai da ke Nigeriya da dukan fadin duniya da zagayowar watan azumin Ramadan.

“Ina mika sakon gaisuwa ta a daidai lokacin da al’ummar Musulmai da ke fadin duniya ke fara shirye-shiryen azumtar azumin watan Ramadan.

“Watan ramadan ya koyar da mu nuna halin kwarai na tausayawa, taimakekeniya karamci da kyawawan dabi’u da sauransu, sannan dama ce gare mu na ziyartar ‘yan uwa abokan arziki da ma sauran al’umma.

“Hakazalika dama ce na tunatar da mu wadanda ba su da ikon ganin watan.

“Sako na ga duk wadanda suka samu damar ganin wannan lokaci mai tarin albarka, musamman ga wadanda ke cikin halin gudun hijira ko tashin hankali, tabbas ina cikin damuwa matuka sakamakon wannan hali na iftila’i da kuke ciki ‘yan uwana.

“Sannan, ina tare da ku a dukkan lokuta walau na tsanani ko na tashin hankali musamman ga wadanda yaki ya daidaita a Gaza da Sudan, da ma sauranan yankunan Sahel.

“Ina kira gare ku, da ku ba da hadin kai kamar yadda na bayar, don samun damar gudanar da azumin watan ramadan cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma ina kira gare ku tare da neman goyon bayanku wajen zaman lafiya da mutunta juna.

Karanta Wadannan:

  • MDD ta saki dala miliyan 5 a cikin shirye-shiryen ambaliyar ruwa, amsa gaggawa a Najeriya
  • FG, States, and LGCs Share N1.703T Revenue for January 2025
  • Supreme Court Acquits Major Convicted of Manslaughter

“A ko wani ramadan, na kan kai ziyara ta hadin kai, tare da yin azumi da al’ummar Musulmi a fadin duniya.

“Wadannan ayyukan su na tunatar da duniya hakikanin halin kwarai na musulunci. Hakanan a kodayaushe na kan samu kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci na ramadan.

“A cikin wannan wata mai alfarma, al’umma na samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan kyawawan dabi’u, ya kamata mu rungumi juna don gina duniya mai cika adalci da zaman lafiya ga dukkan al’umma.

“Ina taya mu murnar zuwan wata mai alfarma ta ramadan.

“Ramadan Kareem”.

Tags: Antonio GuterresDinkin DuniyaMajalisar

Related Posts

News

Police Arrest Four Over Killing of NDLEA Officer

July 24, 2025
News

Two Brothers Marry Same Woman Following Ancient Tradition

July 24, 2025
News

Over 1.3M Students Sit for NECO Exam as CBT Begins

July 24, 2025
News

Muhammed Babangida Accepts Appointment as BOA Chairman

July 22, 2025
News

IGP Says He Can’t Remove Police from Pension Scheme

July 22, 2025
News

Passenger Killed During a Clash Over New Motor Park

July 22, 2025
Load More

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Mondaynuggets

© 2025 MondayNuggets.

The best sites to buy Instagram followers in 2024 are easily Smmsav.com and Followersav.com. Betcasinoscript.com is Best sites Buy certified Online Casino Script. buy instagram followers buy instagram followers Online Casino

Navigate Site

  • News
  • Politics
  • Business
  • Technology
  • Health
  • Sports
  • Entertainment
  • Product Reviews
  • How To’s

Connect With Us on Social Media

No Result
View All Result
  • News
  • Politics
  • Business
  • Technology
  • Health
  • Sports
  • Entertainment
  • Product Reviews
  • How To’s

© 2025 MondayNuggets.